Labarai
Nagodewa Allah har’ila yau daga karshe dai na sake zama gwamnan jihar Adamawa ~Cewar Fintiri.
Gwamnan jihar Adamawa Ahmad Fintiri a lokacin da yake bayyana farin cikinsa A shafinsa na Twitter bayan Hukumar zabe INEC ta bayyana shi amatsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar ta Adamawa Yana Mai cewa…
Alhamdulillah, nasara ce ga al’ummar jihar Adamawa! Har’ila yau na sake zama gwamna ga kowa. Ba za a bar kowa a baya ba kuma ba za a bar kome ba.
An kwashi Yan kallon kafin kawo karshen wannan takaddama tun bayan da Jami’in zaben Prof Hudu ya bayyana Aisha Binani ta jam’iyar Apc amatsayin wacce ya lashe zaben ba tare da an gama tattara Sakamakon zaben ba.