Labarai

Najeriya ta durkushe bayan ta samu cigaba ana bukatar agajin gaggawa ~Inji Atiku.

Spread the love

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kasar ta ci baya sosai kuma ta durkushe, ya kara da cewa akwai bukatar ceto ta a cikin gaggawa.
Atiku ya yi korafi musamman kan abin da ya bayyana a matsayin yunwa a Arewacin Najeriya da ma duk ƙasar nan wanda ya ce na fuskantar mummunan yanayi da damuwa, yana mai cewa manoma, iyaye maza da mata ba za su iya zuwa gona ba.

Da yake magana a karshen mako a jihar Gombe yayin bikin kaddamar da jihohi da shugabancin shiyya ga wata babbar kungiyar matasa a shiyyar Arewa maso gabas da aka fi sani da Nigeria Youth Congress for Atiku, tsohon Mataimakin Shugaban kasa, wanda Hon. Oladimeji Fabiyi, ya kuma koka kan halin rashin tsaro a kasar.
“Yunwar da ake fama da ita a Arewacin Najeriya da kuma duk ƙasar gaba ɗaya ta na fuskantar wani mummunan yanayi mai ban tsoro domin manoman mu, iyayen mu da iyayen mu ba za su iya zuwa gona ba. Noma na daya daga cikin fa’idar da Arewacin Najeriya ke da shi akan sauran yankuna na kasar nan amma kuma, kamar yadda yake a yau kusan babu shi, abin takaici shine yake haifar da mummunan yanayin rashin tsaro a yankin.
“Da kyar za ku iya tuka kilomita goma a kowane yanki na Arewa ba tare da sace ko’ ‘yan fashi da makami sun kawo muku hari ba. Wannan ba abune daya kamata ba a yarda da shi ba, kuma wannan ba lokaci bane na nuna son kai ba ko nuna tausayawa ga shuwagabannin kasa ba, wannan lokaci ne na neman taimako. ”
Yayin da yake godiya ga shugabanni da mambobin kungiyar wadanda suka fito daga jihohi shida na yankin arewa maso gabas na kaddamarwar da kuma goyon bayansu, Atiku ya bukaci matasan Arewa da su kare makomarsu.

“Matasan Arewa suna da hazaka,kokari da hangen nesa kuna da babbar rawar da za ku iya takawa a kan abin da ya shafi yankin ku dan kuma Najeriya ta ci gaba, dole ne ku kare makomarku kuma za ku iya cimma wannan ne kawai ta hanyar tallafawa ɗaya daga cikinku, wanda ya nuna jajircewa ga jin daɗinku, ci gaba da ci gaba. Atiku Abubakar, Dan Asalin Arewa maso Gabas kuma mai kishin da son ci gaban Najeriya na ƙwarai da gaske wanda zai cike gibin.
Fabiyi ya kara da cewa “ni da kaina, ina fata da ace Atiku ya fito ne daga Kudancin Najeriya, da za mu ba shi dukkan goyon bayan da ya dace don ya shugabanci Najeriya, amma ba a makara ba yankin Arewa maso gabas da ma dukkan Arewacin Najeriya su tashi don nuna goyon bayansu ga nasu. ”

Shugaban kungiyar na kasa, Yahuza Shehu, a jawabinsa na maraba ya nuna irin nasarorin da kungiyar ta samu tun kafa ta, yana mai jaddada cewa Atiku ya kasance mafi kyawu kuma mafi cancanta a wajen hada kan kasa mai matukar rarrabuwar kai kamar Najeriya.
“Yankin arewa maso gabas bashi da wani dalili da zai hana wa Atiku goyon baya idan har ya yanke shawarar sa tsayawa takara a 2023.”
Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki, ba kawai a yankin Arewa maso gabas ba har ma a fadin Arewacin Najeriya gaba ki daya da su goya wa Atiku baya idan lokaci ya yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button