Najeriya Ta Rabu Sama Da Zamanin Yakin Basasa – Sarki Sanusi

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya kuma ce mu’amala da Najeriya bayan zaben 2023 ba zai yi sauki ba.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammed Sanusi, ya ce a halin yanzu Najeriya ta rabu fiye da yadda ta kasance a lokacin yakin basasa tsakanin Yuli 1967 da Janairu 1970.
Ya ce an raba Najeriya cikin hadari ta hanyar kabilanci da addini, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan amincin hukumomin gwamnati.
Sanusi ya yi magana ne a ranar Talata a taron shugabannin Najeriya na uku na karrama babban Fasto na Trinity House, Legas, Ituah Ighodalo, wanda ya cika shekaru 62.
“Bana tunanin Najeriya ta kasance a wani wuri mai wahala kamar wannan tun yakin basasa. Muna da kalubalen gina kasa.
“Muna da kasar da ta rabu cikin hadari ta kabilanci da addini.
“Muna da tattalin arzikin da ke cikin rudani, kuma abin takaici, muna da alama muna fuskantar karancin shugabanci a tsakanin shugabannin siyasa,” in ji shi.
Tsohon gwamnan na CBN ya ce, “A watan Oktoban 2022, da yake jawabi a taron zuba jari na Kaduna, na shaida wa ’yan Najeriya cewa, idan wani ya ce musu mu’amala da Nijeriya bayan 2023 zai yi sauki, kada su zabi wannan mutum, kuma ni ke nufi.
“Babu wani tsari da ya dace kamar yadda muka gani a Amurka da Burtaniya cewa sun yi kuskure wajen zabar shugabanninsu. Amma ko kadan jama’a sun san wanda suke zabe. Ina ganin ya kamata mu fara duban dokar zabe tun kafin zabe.
“Muna bukatar mu samar da tsarin da ba za ka iya zuwa kawai ka shiga zaben fidda gwani na jam’iyya ba tare da ka bayyana kanka ga idon jama’a ba. Wannan shi ne abin da ke faruwa a Jam’iyyar Labour ta Burtaniya, da wasu, jam’iyyun Republican da Democrat na Amurka. Akwai bukatar mutane su san wanda suke zabe. A wasu lokuta, doka ta tilasta musu shiga cikin muhawarar jama’a don tattauna batutuwan manufofi.
Ya kara da cewa “Hakika za ku iya zuwa fadar shugaban kasa ba tare da ‘yan Najeriya sun san ko kuna da iya aiki ko hangen nesa don yin aikin ba,” in ji shi.
Sanusi ya kuma yi tsokaci kan yadda ake gudanar da zabe cikin gaskiya, inda ya kara da cewa yin hakan zai karfafa gwiwar jam’iyyun siyasa wajen zabar ‘yan takarar da za su iya yin aikin.
“Muna kuma bukatar mu fara duba tsarin zabe da tsarin zaben da ke da kura-kurai da kuma yadda za a iya inganta shi a dokar zabe. Abu mai mahimmanci shi ne dole ne a sami ingantuwar gaskiya.
“Dole ne a tilastawa INEC ta tattauna batutuwan da suka shafi su da kuma hangen nesan su. Ina ganin idan muka yi hakan za a tilastawa jam’iyyu su ba mu ‘yan takarar da za su iya yin aikin.”