Najeriya Ta Sami Zaman Lafiya Yanzu Fiye Da Shekaru Biyar Da Suka Wuce, Inji Burutai.

Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce Najeriya ta fi koshin lafiya yanzu fiye da yadda ta kasance shekaru biyar da suka gabata.
Ya yi wannan kalami ne a ranar Lahadin da ta gabata a yayin ganawarsa da sojoji da aka yi musu rauni a cikin WIA. Suna karbar magani a Asibitin Sojojin Najeriya 44, Kaduna.
Buratai ya ba da tabbacin cewa, za su sami lada ga kokarin da suke yi na kare al’umma.
Ya jinjinawa sojojin saboda kishin kasa, kwarewarsu da sadaukarwa. “Ina alfahari daku, kun tabbatar da yadda wasu abokan aikinmu da ‘yan Najeriya suke zaune lafiya, kuma ina mai farin cikin cewa muna zaune cikin kwanciyar hankali kuma Najeriya ta fi lafiya yanzu fiye da yadda muka samu shekaru biyar da suka gabata,” in ji shi.
Buratai ya kara da cewa sojojin da suka samu rauni za su samu isasshen lafiya. Babban Hafsan Sojin ya ce za a samar da wuraren nishadi da sauran bukatunsu.