
Matashinnan Sulaiman Isah Panshekara, wanda zai angwance da wata Ba’amurkiya mai suna Janine ya ce nan ba da dadewa za a daura aurensu shi da masoyiyar tasa.
A baya dai an saka bikin nasu ne bayan sallah, amma kuma saboda halin da Duniya ta tsinci kanta aciki na cutar Korona yasa aka daga bikin nasu sai bayan annobar ta tafi.
Sulaiman Isah yayi godiya Jama’ar da suke yimasa addu’a da fatan Alkhairi.