Ilimi

Nan da Makonni 2 Gwamnati ta bude Makarantu Ko mu Tsunduma Zanga Zanga~Dalibai

Spread the love

Kungiyar Daliban makarantun Gaba da Sakandre Sunyi kira ga gwamnatin Tarayya da ta Jahohi su Bude makarantun Gaba da Sakandre nan da Makonni 2 Masu zuwa ko kuma su Shiga Zanga Zanga.

Daliban Sunce Tun watan maris Na wannan Shekarar Aka Kulle makarantu sakamakon, Bullar CoronaVirus a Kasar Nan.

Sannan Sun Nuna Rashin Jin dadinsu kan Hana Kannensu na Sakandre Rubuta Jarabawar WAEC alhali Daliban Zasubi Duk Dokokin da gwamnati da Umarcesu a lokacin Rubuta Jarrabawar.

Sunce Yakamata Gwamnati ta Bude Makarantu kawai Tunda Cutar Covid-19 Ba tada lokacin Karewa Kwana Kusa Inji-Su.

Daliban Sun Yi kira ga Gwamnati kan Ta Biya Albashin Malaman Makarantu da Ba’a Biyasu Hakkokinsu ba, Sakamakon Hutun Corona da Sukeyi- Inji Daliban.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button