Kasuwanci
Nan Da Shekarar 2022 Yawan Talaka A Najeriya Zai Karu lzuwa Miliyan 100 Cewar Bankin Duniya
A jiya, Alhamis, Bankin Duniya ya yi hasashen cewa yawan talakawan Najeriya zai karu daga Miliyan 90 zuwa Miliyan 100 nan shekarar 2022 saboda yadda zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ya taba tattalin arziki kasar.
Rahoton na World Bank yace a shekarar 22 din mutane miliyan 11 ne za su afka cikin Talauci.
Ya ce kafin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19, Mutane Miliyan 2 ne ake tsammanin za su fada talauci a 2020 amma da zuwan cutar, yawan wanda ake tsammanin za su fada talaucin ya karu.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe