Siyasa
Nasara 1 Tal Da APC Ta Samu A Gwamnatinta Itace Ta Daina Dorawa PDP Laifin Gazawarta, Inji Buba Galadima
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa nasara daya da jam’iyyar APC ta samu a mulkinta itace ta daina dorawa PDP Alhakin gazawarta.
Galadima ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Channelstv. Yace kowa zai iya fadin Abinda yake so tunda mulkin Dimokradiyya ake.
Yace amma shi a iya saninsa Nasara 1 tilo da APC ta samu shine ta daina dorawa PDP Alhakin zawarta.