Kimiya Da Fasaha
Nasara Mafi Girma Da Aka Samu A Kimiyya A Shekarar 2024 Ita Ce Yiwa Mutum Dashen Ƙodar Alade.
Wannan mutumin Mai suna Richard Slayman shine mutum na farko da aka fara yiwa dashen Kodar alade a duniya a babban asibitin Birnin Massachusetts.
Kafin yi masa dashen Kodar Richard yana fama da ciwon sugar mai hadari (type 2 diabetes) tare da hawan jini haka zalika ya ɗauki tsawon shekaru yana fama da ciwon ƙoda mafi hatsari wanda ake yiwa laƙabi da ESKD (end stage kidney disease).
A shekarar 2018 an taba yi masa dashen ƙodar mutum amma ba’a yi nasara ba ƙodar ta sake lalacewa, wannan dalilin ne yasa akayi masa dashen ƙodar aladen.
Abin tambayar shine:
- Zaka iya amincewa a dasa maka Kodar alade?
- Ya halatta mutum ya rayu da Kodar alade a gabar mutuwa? Malamai gareku.