Labarai
NDLEA Ta Yi Babban Kamu A Kano..
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi reshan jahar kano ta kama wata babbar mota da ake zargin ta shigo da miyagun kwayoyi.
Shugaban hukumar ta ƙasa reshan jahar kano Dr.Ibrahim Abdul ne ya sanar da manema labarai hakan a shelkwatar dake nan kano.
Dr.Ibrahim Abdul ya ce “Dama mun samu bayanana sirri game da shigowar Motar, hakan yasa mukai shiri na musaman, inda mukabi bayan motar tun daga tittin Zaria”.
Ya ƙara da cewa, binciken da suka gudanar sun gano motar ta ɗauko magunguna ne amma sai aka cakuɗa su da ƙwayoyi.
Daga Amir Sufi