Labarai

Ni Aikin Allah nake Kuma shine zai Kare Ni ~Shekau

Spread the love

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Jama’atu Ahlissunnah Lidda’awati Wal Jihad wanda aka fi sani da Boko Haram, ya yi alfahari a cikin sabon bidiyonsa cewa ba za a iya kama shi ba saboda yana yin aikin Allah ne kuma ‘Zai kiyaye shi.’

“Babu wanda zai iya kama ni, saboda ina yin aikin Allah. Zai kare ni kamar wadanda suke yin irin wannan aiki kuma suka nemi kariyarsa, ”in ji Shekau a cikin dogon bidiyon na tsawon minti 30 a matsayin martani ga sabon yunkurin kamun da sojojin Najeriya suka yi masa da manyan kwamandojinsa.

INNIGERIA ta ruwaito cewa Sojojin Najeriya sun fara farautar Shekau da sauran manyan kwamandojin kungiyar a ranar 11 ga Nuwamba, 2020.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma fada yayin yakin neman zabensa cewa zai murkushe kungiyar Boko Haram cikin kankanin lokacin da ya hau mulki.

A cikin sabon bidiyo, duk da haka, Shekau ya ce babu wanda zai iya kama shi saboda yana yin aikin Allah wanda zai kare shi.

“Babu wanda zai iya kama ni, saboda ina yin aikin Allah. Ne

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button