Ni Ban karbi wata Kwangilar ko sisi ba daga Gwamnatin Bola Tinubu ba ~Cewar Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya musanta cewa yana da hannun jari ko kuma yana da alaka da kamfanin Integrated Logistic Services Nigeria Limited (Intels).
Atiku ya musanta hakan ne a yau ranar Lahadin a shafinsa na X (Twitter) yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya ci gajiyar matakin soke kwangilar da aka kulla tsakanin Intels da gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Tinubu.
Da yake musanta rahotannin, Atiku ya ce ya sayar da hannun jarin sa na Intels, wanda shi ne ya kafa, a watan Disamba 2020 ga iyayen kamfanin, Orlean Investment Group, kuma ya fito fili ya bayyana ficewarsa daga kamfanin a watan Janairun 2021.
A cewarsa, bai ci gajiyar maido da kasuwancin sa ido kan tukin jirgin da gwamnatin Najeriya ta kwace daga hannun Intels ba.
Ya ce, “A watan Janairun 2021, na ba da sanarwar siyar da hannun jarina na Integrated Logistic Services Nigeria Limited (Intels) ga Orlean Investment Group da iyayen kamfanin Intels.