Labarai

Ni ban yarda da hukuncin Kotun korafin zabe ba don haka zan tafi Kotun Koli domin neman Adalci ~Cewar Atiku.

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin tunkarar kotun koli domin ta yi watsi da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.

Atiku, ya ce bai gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, PEPC, da ta tabbatar da shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Da yake magana ta bakin tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Cif Chris Uche, SAN, dan takarar PDP, ya ce ya samu hukunci ne kawai daga kotu ba adalci ba.

“An yanke hukunci amma ba mu samu adalci ba. Anyi sa’a, Kundin Tsarin Mulki ya ba mu damar shigar da kara.

“Wannan ita ce kotun shari’ar farko. Har yanzu muna da ‘yancin kai kara zuwa Kotun Koli, ka ga wannan fafutuka ce ba wai ta wanda muke karewa ba, a’a ga tsarin mulkin kasar nan, don tabbatar da doka da dimokuradiyya.

“Mun kasance muna sa ran samun sakamako wanda zai inganta, karfafa amfani da fasaha don inganta gudanar da zabe, don inganta gaskiya, don inganta rikon amana, ta yadda ‘yan Najeriya za su yi imani da dimokuradiyya.

“Domin ‘yan Najeriya su fito a cikin talakawansu kamar yadda suka yi, don kada kuri’a. Ba ma son ‘yan Najeriya su karaya.

“Akwai wasu abubuwa da ka’idojin doka da ya san cewa muna bukatar mu bincika kuma mun yi imani da cewa idan muka isa Kotun Koli, za ta sami damar yin bitar abubuwa da dama da aka fada a nan a yau.

“Muna da umarnin wanda muke karewa na zuwa Kotun Koli. Don haka, mun nemi bayanan. Mun nemi hukunci. Za mu nemi damar tura bayanan saboda muna da ƙayyadaddun lokaci don tura wannan.

Don haka ana ci gaba da gwabzawa kuma kamar yadda ake cewa, ba a San maci tuwo ba sai an kare,” Lauyan Atiku ya kara da cewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button