Labarai

“Ni Sau Ɗaya Na Kece Raini da Ita” – Mutumin Daya Fashe da Kuka Bayan Yaƙi Yarda da Cikin Gaba da Fatiha.

Spread the love

Wani faifan vidiyo mai cike da abin al’ajabi da mamaki daya karaɗe kafafen sadarwa na zamani wanda har ya janyo martani mai ban dariya daga mutanen dake bibiyar sa.

Faifan vidiyon ya nuna yadda mutumin keta sheƙa gursheƙen kuka, tare da wata budurwa mai ciki.

Mutumin ya bazama tare da carkewa da kuka a fili ɓaro ɓaro yana cewa, bashi bane yayi mata ciki ba.

Mutumin da ba’a bayyana sunan sa ba, ya cigaba da sheƙa kuka tare da fadin, atafau shi sau ɗau ya kece raini da budurwar, ta yaya za’a yi tace harta samu ciki.

To sai dai duk da kukan da yake tayi, budurwar mai ciki ta ƙeƙashe ƙasa tare da riƙe masa ƙugun wando, kuma taƙi sakin sa.Wannan yanayi mai cike da abin ban dariya, yaja hankalin masu kallo.

Hakan ce tasa mutane sukayi cincirindon bayyana ra’ayin su a ƙarkashin vidiyon.

Ga kaɗan daga ciki:

@michaelgove20: “Ku kyale ɗan mutane dan Allah, sau ɗaya suka ƙware fa“.

@abdulsamadadam00: “Ku kyale yaron, domin kana ganin sa kasan sau ɗaya suka ƙware“.

@tcdiegoakukwe: “Wai me yasa koda yaushe gayu suke cewa sau ɗaya suka ƙware ne idan aka samu akasi ciki ya shiga“.

@morshjosh: “ Ya kamata aje a ceci yaron yaron nan.”

@user4524691241806 amrah: “ Ya akayi kuma yake kula da dariya a lokaci guda“.

@Sadifu Yazid: “Dan uwana da yake da aure, shekara wajen biyu kenan shiru kake ji, amma shi wannan bai aure ba amma har ya samu rabo..hmmm“.

Inda ranka kasha kallo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button