Ilimi

NIGERIAN LAW SCHOOL -Dalibai 5 ne Kacal suka Fita da First Class, Inda kuma dalibai 1,067 suka fita da pass.

Spread the love

Nigerian Law School ta fitar da sakamakon daliban da suka zauna Jarabawar karshe domin samun lasisin zama cikakkun lauyoyi.

Kamar yadda Jaridar This day ta ruwaito dalibai dubu daya da dari takwas da Sittin da hudu ne (1,864) suka ci wannan Jarabawar ta karshe wacce ta gudana tun a watan January kamar yadda Director-General din makarantar Prof. Isa Chiroma ya sanar wa manema labarai a ranar lahadi a garin Abuja.

Jaridar Tribune ta bayyana cewa kimanin dalibai dubu biyu da dari biyar da goma sha biyar ne (2,515) suka zauna jarabawar.

A cikin dalibai 1,864 da sukaci jarabawar, biyar daga cikin su ne kacal suka fita da First Class, a yayin da kuma dalibai dari Shida da talatin da biyu (632) suka fadi jarabawar, inda kuma dalibai goma sha bakwai (17) basu zauna jarabawar ba, a yayin da aka rike sakamakon dalibai biyu (2) Sannan dalibai Saba’in da bakwai ne (77) suka gama da Second Class Upper, Sai kuma dalibai dari shida da talatin da uku (633) suka gama da Second Class Lower. Wadanda kuma suka gama da pass marks su kuma adadin su ya kai dubu daya da sittin da bakwai (1,067) wadanda kuma suka gama da Conditional Pass su tamanin da biyu ne (82)
Mr Chiroma ya bayyana cewa: 0.2 per cent ne suka samu First class
3.06 per cent kuma suka samu Second Class Upper 25.17 per cent su kuma suka samu Second Class Lower 42.42 per cent suka samu pass.
3.26 per cent kuma wadanda suke da conditional pass.
25.12 per cent sune suka fadi jarabawar.
0.7 per cent kuma basu zauna jarabawar ba.
0.8 per cent kuma an rike result din nasu.

Dangane da ranar da za’a yimasu Screening da kuma Call to Bar Mr. Chiroma yace za’a sanar.
Bissalam Shehu Rahinat Na’Allah 7th July, 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button