Labarai

Nima sau goma 10 ana kamani ana tsareni a gidan yari, daurin ba sabon Abu bane a zuri’armu ~Inji Tanko Yakasai

Spread the love

Tanko Yakasai, mahaifin korarren mai taimaka wa gwamna Abdullahi Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya ce dangin sa ba sabon abu bane kamawa da tsarewa.

Yakasai ya shiga hannun jami’an ne a ranar Juma’a bayan da ya soki yadda gwamnati ke tafiyar da harkokin tsaro.

Yakasai, wanda ya yi magana a yayin zantawa da Daily trust ta wayar tarho, ya ce bai yi mamakin kame dan nasa ba.

Dattijon ya kasance daga cikin ‘yan siyasar da gwamnatin soja ta Muhammadu Buhari ta tsare a shekarar 1983, bayan juyin mulkin da ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.

Yakasai ya kasance jami’in tuntuba na shugaban kasa (PLO) a karkashin Shagari

A wata sanarwa a ranar Asabar da yamma, DSS ta ce Yakasai na tsare, tana mai cewa an tsare shi ne saboda wasu laifuka ban da “bayyana ra’ayi a kafafen sada zumunta”.

Amma babban dattijon ya dage cewa ƙaramin Yakasai bai aikata wani laifi ba sai kawai ya soki gwamnati.

Dan siyasar na Jamhuriya ta Farko ya ce ‘yan uwa suna jira su ga matakin da DSS za ta dauka zuwa karshen Litinin, yana mai cewa wannan shi ne zai yanke hukuncin matakin da za su dauka a gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button