ƙara-ƙaƙa-ƙaƙa — Wahala kenan, yayin da wani yaro ɗan shekara huɗu, yayi amfani da katin bankin mamansa ya sayo Alewa ta Naira miliyan ɗaya.

Wani yaro ɗan mitsitsi wanda baifi shekara huɗu da haihuwa ba, ya saka mamansa a jarfa, ƙwarai kuwa, jarfa iya jarfa.

Domin zancen da ake yi yanzu haka, yasakata cikin mummunan bashi wanda Allah kadai yasan ranar da zata biya.

Hakan ya faru ne sakamakon sayo alewar tsotsa da yayi harna zunzurutun kuɗi kimanin Naira Miliyan guda daga manhajjar Amazon, shagon saye da sayarwa na yanar gizo gizo.Mahaifiyar yaron ce ta tabbatar da cewa yaron ya kashe zunzurutun kuɗi kimanin Dalar Amurka $2,618.85 wanda yayi daidai da Naira miliyan N1,062,802.00, wanda bashin ne data ciwo da zummar biya da kuma kula da karatun ta yaron.

Amma saboda wannan katankatana da yaron ya aikata, ya jefata a cikin halin la-ila-ha-ula-i, inda tace biya yanzu ya zama mata ƙarfen ƙafa, tunda daman ita bamai hali bace.

Tana zaune, kawai sai taga anata zuwa ana jibge mata akwatunan alewa mai taken SpongeBob SquarePant, acikin mamaki kawai saita bisu da kallo, domin tasan ita dai bata siya da kanta ba.

Bugu da ƙari, yanayin sayen da yaron yayi mata, irin salon nan ne, da ba’a zuwa a dawo, ko a komar da kaya. Saboda haka dole ta amsa ko tanaso, ko bata so. Kamar yadda jaridar New York post ta ruwaito.

To sai dai kuma, abin nata daga ƙarshe ya zame mata gobarar titi a Jos, domin tuni ƴan uwa da abokan arziki suka buɗe mata wani asusun tallafi na GoFundMe, inda tuni a dai dai lokacin da muke haɗa wannan rahoton ya samu nasarar tara mata zunzurutun kuɗi mai yawan dala dubu uku da ɗari shida da saba’in da biyar wato kimanin Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar da biyu da ɗari biyu da ashirin da tara.

Wannan ƙalubale ne ga iyaye maza da mata da

suke barin katin bankinsu ko wayoyin su dake ɗauke da asusun ajiya kona siye da siyarwa a hannun ƙananan yara da basu san komai ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *