Gareku Samari, yawan kashe wa mace kudi kafin aure yana kawo babbar matsala, in ji wata budurwa Mai suna Hafsat.

Wata matashiya mai suna Hafsat Sama’ila Mabai ta shawarci samari da su rage kashewa ‘yanmata kudi kafin su auresu.

Matashiya Hafsat ta ce kashewa Budurwa kudi kafin aure yana haifar da gagarumar matsala.

Sai dai kuma bata zayyana irin matsalolin da kashewa Budurwa kudi kafin aure suke haifarwa ba.

Hafsat Sama’ila Mabai ta rubuta a shafinta na Twitter kamar haka “🗣🗣 🗣 Samari kuna ji koh, yawan kashe wa mace kudi kafin aure yana kawo babbar matsala”.

Sai dai kuma tuni samari sukai ta maida mata da martani, in da wasu ke ganin shawarar tata a Matsayin abar ayi amfani da ita ce, wasu kuma na ganin shawarar tata a Matsayin gurguwa marar kafafu.

Samari da yawa sun ce su fa ‘yanmatan yanzu muddin kace ba za ka kashe musu kudi ba to tabbas kana ji kana gani za su sami wani saurayin su ajiyeka a gefe kana zare ido.

A Saboda haka ne ma suke ganin wannan shawarar ta Hafsat ba ta da wani amfani agaresu face su watsa ta kwandon shara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *