Jackie Chan ya gama shiri tsaf domin sadaukar da duka dukiyarsa ga masu ɓukata, inda zai bar ɗan sa guda ɗaya tilo babu ko sisi.

Jackie Chan

Shahararren ɗan wasan kwaikwayon nan dan kasar China Jackie Chan, ya sanarwa da manema labarai burin sa daya ke fatan cimma na ganin ya bada dukiyar sa gabaki ɗaya ga gidauniyoyi domin tallafawa masu ɓukata da zarar ya mutu, wanda hakan zai bar ɗansa, Jaycee a matsayin faƙiri.

Tashar NewsAsia ta rawaito Jackie Chan yana cewa, ”Idan ɗan dana haifa ya cika namiji, zai tsaya ya nemi na kansa. Idan kuwa ba haka ba, nasan dukiyar tawa ko bayan na mutu lalata ta zaiyi.”

Jackie Chan da ɗansa

Jackie Chan ya ƙara da cewa, yaso ace lokacin da Jaycee yana ɗan ƙarami sosai, ya shigar dashi wajen horon sojoji, domin ya horu, ya zama jarumin gaske.

A satin daya gabata ne dai, raɗe raɗi ya dinga yawo cewar wai Jackie Chan mai shekara hamsin da shida, ya mutu ta sanadiyyar bugun zuciya wanda har yasa “RIP Jackie Chan” (Allah ya jiƙan ka Jackie Chan) yayi tashe sosai a dandalin sada zumuntar nan na Twitter.

Uba da Ɗa, Jackie Chan da Jaycee

To sai dai nan da nan Jackie Chan ya fito ya ƙaryata wannan rahoto ta shafinsa na facebook m, inda ya tabbatar wa magoya bayan sa cewar yana raye kuma cikin koshin lafiya.Jackie Chan ya ƙara fatattakar jita jitar da cewa: “Nifa ban mutu ba gaskiya, kawai dai na shiga aiyuka ne da suka sha kaina”.

“Nidai fatana ace, kafafen yaɗa labarai da kafafen sada zumunta na zamani zasu maida hankali wajen kawo rahoto akan abubuwan da zasu amfani jama’a da kuma aiyukan jin ƙai, maimakon gulma, tsegumi, da tsugudidi.

Jaycee

Hakan yafi alfanu fiye da komai. Wannan jita jita saida tasa shahararren ɗan wasan kwaikwayon nan na Hollywood, wato Will Smith maganar ta shigar dashi damuwa, wanda hakan yasa ya aika da saƙon taya jaje ga yan uwana da abokan arziki ta yanar gizo”.

A yanzu haka, Jackie Chan tare da haɗin gwuiwa da wasu manyan gidauniyoyi na duniya suna nan sunata raba kayan tallafi ga waɗanda iftila’in girgizar ƙasar Japan da Tsunami suka yiwa mummunar ta’adi watan daya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *