Nishadi

Magani A Gonar Yaro: Yin rawa yana Maganin Ciwon Zuciya, sannan yana hana cutar mantuwa da ruɗewa yayin tsufa

Spread the love

—Rawa tana ƙara buɗe ƙwaƙwalwa da tunanen dan Adam Kamar Yadda Professor Tim Watson da Dr. Andrew Garrett dukan su daga Jami’ar Hertfordshire suka bayyana.

—Yin rawa Yana Maganin Ciwon Jiki da kuma gajiya, Kamar yadda wani bincike da aka gudanar a Jami’ar Washington, St. Louis School of Medicine a Shekarar 2007 ya bayyana.

—Yin Rawa yana hana ciwon ƙafa a lokacin da mutum ya tsufa, kamar yadda Dr. Paul Dougall na Jami’ar Strathclyde ya bayyana a wani bincike da yayi a Shekarar 2010.

—Yin Rawa yana Maganin Ciwon Wuya da Ciwon Baya kamar yadda Anna Duberg, Na Sweden’s Center for Health Care Sciences ya bayyana.

—Yin rawa yana yaye Cutar damuwa (Depression) Kuma yana saka Nishadi da farin ciki.

—Yin rawa yana hana cutar Mantuwa (rudewa) a lokacin da tsufa ya kama mutum, Kamar yadda Debbie Duignan ya bayyana a wani karatu da yayi a Perth Western Australia a Shekarar 2009.

—Sannan Yin rawa yana Maganin Ciwon Zuciya, kamar yadda binciken American Heart Association, 2009 ya tabbatar, da Kuma binciken da Heart Care Sukayi a Kasar Italy a Shekarar 2006.

—Yin rawa yana rage Ƙiba, yana ƙara lafiya da ƙarfin Jiki, yana washe ƙwaƙwalwa (Brain’s Refreshment)

Shehu Rahinat Na’Allah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button