Yadda aka sassaɓamun kamanni na a ofishin ƴan sanda- Mr Macaroni.

Shahararren ɗan wasan barkwancin nan ɗan kudancin Najeriya wanda aka fi sani da Mr. Macaroni ya bayyana irin halin la-ila-ha-ula-in daya fuskanta yayin da ƴan sanda suka ƙwamushe shi a yayin zanga zangar nan ta Endsars da akayi a Najeriya a kwanakin baya.

Mr. Macaroni ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunci ta twitter cewa:

“Lokacin da nake Police Station ta Adeniji, har bani in baka “yan sandan suka dinga yi dani wajen jibga ta. Har kiran juna suka dinga yi wai yau zasu daki ‘Mr. Macaroni’, ɗaya daga cikinsu sai da ya faɗamin cewa, idan nan gaba kaji an ce ɗan sanda, saika gudu. Wani kuma cewa yayi dani, da’ace jama’a basu sanka ba, to dana kashe ka!

Tun daga nan , naɗauki alkawarin cewa, zan dinga amfani da duk wata kafa dana samu, domin nuni da halin cin zali da yan sandan Najeriya ke yi.

“Idan zasu iya yiwa mutumin da aka sani, kayi tunanin me zasuyi ga adadin dubunnan mutane da sukeyi yiwa wanda jama’a basu sani ba”. Inji Mr Macaroni.

To sai dai , koda Sashen BBC na Pijin ya tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya maida martani da cewa baida masaniya abisa wannan zancen maras tushe, balle makama.

Mr. Macaroni dai yayi kaurin suna wajen wasan barkwanci, kuma yana da magoya baya da yawa saboda yadda yake ilmantarwa, nishadantarwa a cikin salon barkwanci.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *