Labarai
Nnamdi Kanu Ya Fara Gajiyane? Ina Ji Kamar ln Bar Fafutukar Nan Ta Kafa Kasar Biafra Inji Nnamdi.
Shugaban kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya bayyanawa magoya bayansa cewa shifa wani Lokacin ji yake kamar ya hakura da wannan fafutukar.
Ya bayyana hakane a wasikar da ya aikewa mabiyansa ta hannun me magana da yawunsa, Emma Powerful inda yace yana bin sahun annabi Isa(AS) ne. Mun ruwaito muku Kanu na martanine kan kisan ‘yan kungiyar da DSS suka yi.
Yace jinin wanda aka kashe bai zuba a banza ba dan ba zasu daina fafutuka ba har sai kasar Biafra ta kafu. Yace maimakon daina fafutukar zai ci gaba da yakar harin da jami’an tsaron Najeriya ke kaiwa kungiyar tasu.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe