Nnamdi Kanu ya Gargadi Membobin IPOB Kan Yarbawa.
Shugaban Kungiyar Nan Mai Fafutukar Kafa Kasar Biafra Nnamdi Kanu, ya umarci Mambobin Kungiyarsu Ta IPOB, da ta daina Aibata Yarabawa a lokacin Gudanar da Al’amuransu.
Kanu ya umarci daukacin ma’aikatan kungiyar na kafofin watsa labarai, da su yi biyayya da umarnin shugabanta, Mazi Nnamdi Kanu, tare da dakatar da duk wasu hare-hare a kan Yarbawa.
IPOB a cikin wata sanarwa da Shugaban Direktan Harkokin Kasar, Chika Edoziem, ya umarci dukkan ma’aikatan kafofin watsa labarai, da su yi biyayya ga umarnin shugabanta, Mazi Nnamdi Kanu, tare da dakatar da duk wani harin da suke Kaiwa kan Kabilun Yarabawa kamar yadda abaya Suke Farmasu- Inji Shi.
Kanu ya Sanar da hakan yayin watsa shirye-shiryensa na ranar Lahadi, 19 ga Yuli, 2020, ya ce duk hare-haren da ake kaiwa kan Yarabawa ya kamata su daina. Nan da nan, Direktan Kungiyar ya Jaddada Mubaya’arsa kan Kalaman Shugaban na Dakatar da Kai hare hare da aibatata Yarabawa a Yankin.
“Saboda Haka duk Ma’aikaci ko mamban kugiyar ya Tabbatar ya amsa kiran Shugaban Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas