NNPP ba ta da dan takarar Gwamna a Kano, muna son a bayyana Gawuna a matsayin zababben Gwamna – APC ta fadawa Kotu
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bukaci kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano da ta bayyana zaben ranar 18 ga watan Maris na jihar, a matsayin wanda bai kammala ba.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da Abba Kabir-Yusuf, dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ya samu kuri’u 1,019,602 inda ya kayar da dan takarar APC, Nasiru Gawuna, wanda ya zo na biyu da kuri’u 890,705.
A cikin karar mai juzu’i biyar da ta shigar a ranar 9 ga watan Afrilu, APC ta yi zargin cewa Kabir-Yusuf bai cancanci tsayawa takara ba saboda ba ya cikin rajistar jam’iyyar da aka mika wa INEC.
Jam’iyyar APC ta kuma bayyana cewa jam’iyyar NNPP ba ta samu rinjayen kuri’u na halal ba a zaben.
Jam’iyyar ta ce wasu daga cikin kuri’un da aka baiwa NNPP ba su da inganci, inda ta ce idan aka cire su daga jimillar kuri’u, APC ce ke da mafi yawan kuri’un da aka kada.
APC ta ci gaba da cewa, kwamishinan zabe na Kano ya yi kuskure da ya ayyana Kabir-Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta kara da cewa tazarar shugabanci bai wuce kuri’un da aka soke ba.
Don haka jam’iyyar ta yi roko ga kotun da ta bayyana cewa NNPP ba ta da dan takara a zaben.
APC ta kuma roki kotun da ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
A wani bangaren kuma, APC ta bukaci kotun da ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
A cewar NAN, Gawuna bai shiga cikin takardar ba.
Wadanda ake kara a karar sun hada da NNPP, Kabir-Yusuf, da kuma INEC.
A cikin wata sanarwa bayan zaben, Gawuna ya ce ya dauki sakamakon zaben da gaskiya.
A halin da ake ciki, Abdul Adamu-Fagge, mashawarcin APC kan harkokin shari’a, ya shaida wa NAN cewa, kotu ta amince da bukatar da ta baiwa jam’iyyar damar duba kayan zaben gwamna a dukkan kananan hukumomin jihar 44.