Obaseki Ya Mika Godiya Da Jin-jina Ga Kwankwaso Da Gwamna Wike..
Zababben gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar PDP Godwin obaseki ya mika sakon jinjina ga tsohon gwamnan jihar kano Dr Rabiu Musa kwankwaso da abokin aikinsa gwamnan jihar Rivers Nelson wike bisa jajircewar su wajen tabbatar da nasarar jam’iy,yar PDP a jihar Edo.
Sannan ya mika godiya ga iyayen jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasar Najeriya chief olusegun Obasanjo, bisa harbo makami mai linzami irin na siyasa da suka rinka yi yana warware makircin da jam iyar APC ta shiryowa jihar ta Edo.
Idan baku manta ba a ranar Asabar din da ta gabata ne aka fafata a zaben gwamnan jihar ta Edo Tsakanin ‘yan takarkaru daban-daban a jam’iyyu maban-banta, fafatawar da tafi ɗaukar hankali ita ce tsakanin Gwamna Godwin Onaseki na Jam’iyyar PDP da kuma pastor Eze Iyamo na Jam’iyyar APC.
A jiya lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Gwamna Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Daga Kabiru Ado Muhd