Labarai

Obasonjo Babanmu Shine Jagoranmu, Dole Mukoya Daga Gare shi -Tambuwal.

Spread the love

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato a jiya ranar Asabar ya baiyana cewa duk da barin Tsohon Shugaban kasa Obasonjo ofis shekaru 13 da suka gabata, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo har yanzu ya kasance mai dacewa da anemi shawarwari kan batutuwan shugabanci da kalubalen kasar ke ciki daga gare shi.

Tambuwal, a lokacin ziyararsa ga Tsohon Shugaban kasar ya bayyana Obasanjo a matsayin mai fada a ji, ya ce shugabannin kasar za su ci gaba da koyo daga dimbin iliminsa don magance matsalolin shugabanci da kalubalen da kasar ke fuskanta a yau.

A cewar Tambuwal: “Kun san Baba shi ne jagoranmu, shugaba. Kuma koyaushe yana da kyau mu zo mu duba halinda yake ciki mu yi masa mubaya’a mu yi masa bibiya kan batutuwa da yawa na shugabanci;
shi ya sa muka zo wannan gaishesa a wannan maraice.

Kuma, mun kawo masa gaisuwa ne a madadin kyawawan Al’ummar jihar Sakkwato. Tambuwal ya kara da cewa zamu mu sha daga yawan gwanintarsa ​​da kuma tushen iliminsa da hikimarsa kan al’amuran yau da kullun na shugabanci da kalubalen yau.

Mun yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba shi lafiya mai kyau kamar yadda na sadu da shi a yau, kuma ya ce allah ya tsaremu daga wannan annoba ta Covid-19.

A karshe gwamnan yayi magana kan kokarin gwamnatin sa na maido da zaman lafiya a jihar ta sakkwato…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button