Oshiomale Yace ‘Yan Nageriya suna ganin Kamar ta karemin don kawai APC ta Fadi Zabe a jihata ta Edo
Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, a ranar Laraba ya ce kayen da jam’iyyarsa ta Apc ta sha ba ta shafe shi ba a zaben gwamnan da aka yi a ranar 19 ga Satumba a Jihar Edo. Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin hirarsa ta farko tun bayan kayen da jam’iyyar ta sha a zaben a gidan TV na GEE Africa TV.
Ya ce, “Ina son in gode wa kowa. Na tabbata mutane da yawa suna tsammanin cewa ta karemin Wanda Hakan Kuma Rashin sanin ikon Allah ne
a Lokacin da Allah yace sai Kai to Babu Mai hanawa shi ba ruwansa Ba tare da la’akari da sakamakon zabe ba ko kuma wani tsari na tsari,
kuyi imani da Allah kuma kuyi imani da kasarmu. Allah ya albarkace ku duka. Baki daya Inji Oshomale.
Idan baku manta. Ba dai ” A shirye-shiryen zaben ranar Asabar din da ta gabata, Oshiomhole ya yi alfahari da cewa zai koyar da Godwin Obaseki, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP kuma gwamnan jihar mai ci, babban darasi a siyasa. Amma lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta karanta sakamakon zaben a ranar Lahadi, amatsayin Obaseki ya lashe zaben na Gwamnan Edo sai Kuma
ya rufe bakin Oshiomhole da sauran jiga-jigan APC ciki har da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya yi hasashen faduwa a gare shi. . Obaseki ya samu kuri’u 307,955 inda ya kayar da Osagie Ize-Iyamu, dan takarar APC, wanda ya samu kuri’u 223,619. Obaseki dai da can can Yana Cikin Jam’iyar APC Amma suka hanashi Shiga Zaben fidda gwani Suka ce Gwamnan bai cancanci tsayawa takarar zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ba bayan ya samu sabani da Oshiomhole kan batun gudanar da jihar Edo. Amma Obaseki ya sauya sheka zuwa PDP inda ya tsaya takara kuma ya ci zaben…