Rahotanni
Osinbajo zai zama shugaban ƙasar Najeriya a shekarar da muka shiga ta 2021, in ji wani Fasto Jagoran Kiristoci a ƙasar Ghana.
Wani fasto da ke zaune a kasar Ghana, jagoran Nigel Gaisie, ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa a 2021.
Gaisie, wanda shi ne wanda ya kirkiro gidan Mount Chapel ya yi wannan hasashen ne yayin hidimarsa ta ranar Alhamis, kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo zai zama shugaban kasa,” in ji shi.
Fasto Gaisie ya kuma yi yi hasashen matsala a Masarautar Ashanti ta Ghana.
Ya ce: “Na ga duhu kewaye da masarautar Ashanti.”
Faston ya ba da tabbacin zaman lafiya a duk duniya.
Ya kuma ce wani sanannen mai wa’azi zai mutu a 2021.
“Duniya za ta ji daɗin zaman lafiya, amma Amurka za ta sami harin ta’addanci,” in ji shi.