Labarai

Osinbanjo ya Cika Shekaru 64 Banyi nadamar Zaben Osinbanjo a Matsayin mataimakina ba ~inji Buhari

Spread the love

A wata sanarwa ta musamman da mataimakin Shugaban Kasa Kan harkokin yada labarai ya fitar Malam Garba Shehu na Cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Mataimakinsa Yemi Osinbajo a matsayin “amintaccen kuma mai sadaukarwa wanda ba iya kwazo ba kawai ya kasance mai karfin gwiwa da kwazo a aikinsa.”

A sakon da ya aike don taya mataimakin shugaban kasar murnar cika shekaru 64 a ranar Litinin 8 ga Maris, Shugaba Buhari ya ce “Ina alfahari da na zabi Osinbajo a matsayin abokin takarata kuma ya yi kyakkyawan bayani game da kansa tun Lokacin da tafiyarmu ta fara a 2015.”

A cewar Shugaban, “Mataimakin Shugaban kasa mutum ne mai sanyin jiki wanda ya fifita sha’awar Najeriya sama da sauran maslaha.”

Shugaba Buhari ya kuma lura cewa “Mataimakin nasa Osinbajo hazikin dan siyasa ne wanda ke nuna kwazo da hazaka wajen gudanar da ayyukansa.”

Ya yi masa fatan shekaru masu tarin yawa da kuma ci gaba daga Allah Madaukakin Sarki.

Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa
(Kafofin watsa labarai & Jama’a)
Maris 07, 2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button