Labarai
Pantami: Allah yasa mutuwa Hutu ce, da Yana raye da yanzu Yana Fadar Aso Rock Villa Yana Rusa kuka ~PDP Vanguard.
Wani shafin Jam’iyar PDP a manhajar Twitter sun rubuta tare wallafa Hoton Minisatan Sadarwa Dr Ali Isa Pantami sun Kuma Caccaki malamin a fakaice Kan kinyin magana a Batun batan ‘yan Makarantar kagara da Kuma ‘yan matan Makarantar jangebe da aka sace a jihar Zamfara.
rubutun Yana Cewa Allah ya jikan Marigayi Sheikh Dr Isa Pantami Muna fatan ya ci gaba da hutawa a cikin dausayin Allah Madaukakin Sarki.
Da’ace yana raye, da yanzu Yana fadar Ado Rock Villa yayi zaman dirshan yana zubar da hawaye yana tunatar da Shugaba Muhammadu Buhari Kan ya ceci daliban kagara da Kuma ‘yan matan Jangebe.
Shin Kuna kewar marigayi Pantami!?