Rahotanni
PDP Na Murna Saboda Dodonsu Magu Yanzu Ya Bar Ofis Hadimin Shugaban Kasa, Sagay.
Daga Comr Yaseer Alhassan
Hadimin shugaban dake baiwa shugaban shawara kan yaki da rashawa farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa, PDP na murna saboda Dodonsu, Ibrahim Magu yanzu baya Ofis.
PDP dai ta yi kira ga shugaban kasa,Muhammadu Buhari da ya hukunta Magu saboda zarge-zargen da ake masa wanda suka nuna cewa yaki da rashawar da aka yi akwai son kai da kuma fada da abokan gaba a karkashinsa.
Saidai da yake mayar da Martani a hirar da yayi da Independent, Itse Sagay ya bayyana cewa dole PDP ta fadi haka tunda Magu ya tura da yawa daga cikin membobinta zuwa gidan yati wasu kuma suna kan hanya.
Yace dolene jam’iyyar ta yi murna idan ta ji Magu bayanan.