Siyasa

Ra’ayin Jama’a Shine Zai Zama Tushen Gudanar Da Mulkin Ƙasa, Inji Comrade Sani Daitu.

Spread the love

Kowani mutum nada Ƴancin takarawa cikin sha’anin mulkin ƙasar sa da kansa ko ta hanƴar wani wakili da ya za6a.

Duk Ɗan ƙasa na da ƴancin yin irin aikin da yake so a ƙasar sa.

Ra’ayin jama’a shine zai zama tushen gudanar da mulkin ƙasa.
Sannan kowa zai bayyana ra’ayin nasa ne ta hanƴar gudanar da sahihin za6e, wanda ake gudanarwa a wani lokacin da aka ambata. Kuma kowa na da Ƴancin wannan za6e a asirce ta hanƴar kaɗa ƙuri’a.

Kowani Ɗanƙasa nada Ƴancin a tabbatar ana kare masa.

  • Rai
  • Dukiyar sa
  • Addinin sa
  • Mutuncin sa.

Muna kira da bubban murya Gwamnati ta tsaya ta kare Haƙin Bil’Adama. Kulun ana salwantar da rayuka da dukiyoyi, ana raba Iyalai da muhallin su, Ana cin zarafin Ƙananan Yara da Mata.

Muna kira ga Al’umma da kada suyar da su dauki doka a hannun su. Kowacce ƙasa tanada dokoki na kare haƙƙin Ɗan Adam a Kundin tsarin mulki na ƙasar ta. Wajibine a garemu mubisu sau da ƙafa.
Zagin shuwagabanni bazai fishe mu ba. Muyi amfani da dokokin ƙasa don tabbatar da ammana abinda muke buƙata.

Comrade Sani Musa Daitu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button