Rahotanni
Rahama Sadau Ta Yi Zazzafan Martani Ga Wani Da Yace Ita Da Aure Har Abada.
Jarumar fina-finai Rahama Sadau ta mayar da martani ga wani mai amfani da shafin tuwitta wanda yace ita da aure har abada.
Mai shafin tuwitar mai suna Shegen Kauye ya wallafa wani gajeren bidiyon Rahama Sadau mai tsayin dakika goma wanda take cashewa a wajen wani shagali tana sanye da kayan da suke bayyana surar jikinta.
Ga abinda yace “Allah Ya shirya keda Aure kam Har abada 😒.”
Sai dai kuma da alama kalaman na Shegen Kauye basu yiwa Jaruma Rahama Sadau dadi ba, domin kuwa hakan ya fusata Jarumar ta yi zazzafan martani akan maganar.
Jarumar ta ce idan tayi auren sai ya kashe kashe, ta kuma kira shi da sunan jahili..
Ga abinda tace “Idan nayi auren sai kazo Ka kashe… Jahilii!!! 😤”.