Ƴan ta’adda sun nemi kuɗin fansa naira miliyan 30 bayan sun karɓi naira miliyan 10 daga dangin waɗanda su ka yi garkuwa da su

Ƴan Ta’adda Sun Nemi Kuɗin Fansa Naira Miliyan 30 Domin Su Saki Ma’aikatan Aikin Jinya Da Su Ka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Kaduna, Bayan Sun Karɓi Miliyan 10

Ƴan ta’adda sun yi garkuwa da ma’aikatan jinya guda biyu a babban asibitin Doka, ƙaramar hukumar Kajuru jihar Kaduna, sun nemi a basu naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa kafin su sake su.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma (NANNM) reshen jihar Kaduna, Comrade Ishaku Yakubu ya faɗawa ƴan jarida tun da farko ƴan ta’adda sun karɓi naira miliyan 10 daga dangin waɗanda su ka yi garkuwa da su domin su sake su.

“Tun da farko masu garkuwa da mutanen, sun nemi a basu miliyan goma da katin waya na naira dubu hamsin da kuma wayoyin kira tecno guda huɗu, bayan sun karɓi naira miliyan gomar ta kuɗin fansa, sai suka sake kiran waya domin a ƙara basu waɗansu kuɗaɗen”

“Ita kanta miliyan gomar da aka basu da farko ƴan uwa da abokanan arziƙi ne suka yi karo-karo” inji Comrade Ishaku Yakubu

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *