Ƴan ta’adda sun yi sansani a dajin Kano- A cewar Ganduje

Ƴan ta’adda sun yi sansani a dajin Kano- A cewar Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ankarar da al’ummar jihar, biyo bayan zargi da ake yi na wasu ƴan ta’adda sun yi sansani a dajin Falgore.
Ganduje ya yi wannan jan hankalin ne a ranar Alhamis a loƙacin daya ziyarci hedikwatar tsaro ta ƙasa a Abuja, wanda ya haɗu da shugabannin hafsoshin tsaro akan yadda za a inganta tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa ƴan ta’adda sun yi sansani a dajin domin su kai hari cikin jihar.
” A yau na ziyarci wannan wurin ne domin na jajantawa rundunar sojojin Najeriya akan mutuwar tsohon hafsan sojojin ƙasa Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan sojoji guda 10 da suka riga mu gidan gaskiya”
“Sannan na zo nan ne domin na nemi taimakon rundunar sojojin Najeriya da su taimakawa jihar Kano saboda ƴan ta’adda sun ɓuya a wasu dazuzzuka a jihar”
A daga na shi ɓangaren, sabon hafsan sojojin ƙasar Najeriya, Farouk Yahaya ya yi alƙawarin kai ziyara dajin domin ganin hanyoyin dayakamata su bi su gudanar da aikinsu”
Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *