Ɗaya daga cikin limaman Ka’aba ya ziyarci Zulum sannan ya yaba da salon mulkinsa

Ɗaya Daga Cikin Limaman Ka’aba Ya Ziyarci Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum Sannan Ya Yaba Da Salon Mulkinsa

Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari malami a jami’ar Saudiya sanna ɗaya daga cikin limaman da su ke jagorantar sallar Juma’a a Haramin Makkah ya ziyarci gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Limamin ya ziyarci gwamnan a gidan gwamnati a yammacin ranar Laraba

Imam Bukhari shine shugaban tsangayar koyar da harshen Larabci a jami’ar Ummul Qura a Makkah, ya ziyarci birnin Maiduguri bayan ya samu goron gayyata daga Dr. Mohammed Kyari Dikwa shugaban gidauniyar Al-Ansar kuma wanda yanzu ya ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a Maiduguri.

Limamin Ka’abar, a loƙacin daya ke ganawa da Zulum ya yaba da irin yadda karamcin al’ummar Borno da kuma tsohon tarihin karatun Qurani a jihar. Ya bayyana Borno a matsayin wacce ta yi suna a duk faɗin duniya saboda yawan adadin mahaddatan Quranin da suke cikinta

Farfesa Bukhari wanda Dr. Dikwa ya fassara jawabinsa cikin harshen Turanci, ya bayyana farin cikinsa da irin salon mulkin Zulum sannan tun daga ƙasar Saudiya suna sanya ido dangane da ayyukan alherin daya ke aiwatarwa a jihar.

“Farfesa Bukhari ya yi matuƙar jin ɗaɗi haɗuwa da kai, sannan tun a shekarun baya suna sane da irin aikace-aikace da ka ke gudanarwa a jihar, dan haka ya yi farin ciki dana ya zo ya haɗu da kai sannan ganewa idanuwasa irin cigaban da aka samar a jihar Borno” In ji Dr. Dikwa.

Gwamna Zulum ana shi ɓangaren, ya bayyana daɗaɗɗiyar alaƙa da gwamnatin Borno ta ke dashi da mutanen ƙasar Saudiya

“Haƙiƙa, Ɗaya daga cikin limaman Ka’aba ya ziyarci Maiduguri, wannan babban abin farin ciki da alfahari ne ga ɗaukacin al’ummar musulman jihar” inji Zulum.

Sannan ya nemi ƙasar Saudiya data tallafawa gwamnatinsa wajan koyar da harshen da ilmin addinin musulunci a jihar

Zulum ya ƙara neman goyon baya ƙasar Saudiya akan yadda za a daƙile tsatstsauran ra’ayin addinin Islama a jihar saboda ta samu zaman lafiya mai ɗorewa.

Daga ƙarshe, gwamna Zulum ya yi bayani akan yadda al’ummar Kanuri suka samo asali daga ƙasashen Larabawa kafin su yi hijra zuwa Borno

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *