A hubbaren gidan sarkin Kano za a binne mai babban ɗakin Kano

A hubbaren gidan Sarkin Kano za a binne Mai Babban Ɗaki

Majalisar masarautun jihar Kano ta ce ana dakun isowar gawar Mai Babban Ɗakin Kano Hajiya Maryam Ado Bayero a ranar Lahadi bayan Sallar Magariba.

Mai Babban Ɗakin Kano ta rasu ne a ranar Asabar a ƙasar Masar.

Sanarwar da majalisar masarautun Kano ta fitar da ke dauke da sa hannun Madakin Kano ta ce a ranar Litinin misalin ƙarfe 11:00 na safe za a yi jana’izarta a ƙofar kudu fadar Sarkin Kano

“Za a binne ta ne a hubbaren gidan Sarkin Kano,” in ji sanarwar.

Hajiya Maryam Bayero matar marigayi Sarkin Kano Ado Bayero mahaifiya ce ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da kuma Sarkin Bichi Nasir Ado Bayaro

BBC-Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *