An Sami Rijiyar Man Fetur A Jihar Sokokto: Mun waye gari a safiyar yau Lahadi rijiyar gidanmu ta cika da ɗanyen man fetur (crude Oil) – in ji Hon. Babangida Tambari.

Hon. Babangida Tambari ya sanar da cewa abin alkhairi ya samu a jihar su ta sokoto, kuma a karamar hukumar su ta Yabo, a cikin garin su da’gawa inda suka wayi gari a safiyar yau lahadi rijiyar Gidan su ta cika da dan’yen man fetur (crude Oil).

Hon babangida tambari ya ce yanzu haka mutane na ta tururuwar zuwa Gidan don gani da idanun su domin tabbatar da maganar.

Hon babangida tambari ya kara da cewa yanzu haka wannan rijiya na nan a cikin gidan su, yanzu haka mutane ma nan suna ta debowa.

Hon Babangida tambari ya ce ya rantse da Allah wannan magana gaskiya ce.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *