Babbar magana: Ba da sanin Buhari aka sauke tsohon sufeton ‘yan sanda ba – In ji wata Majiya.

Wasu makusantan Shugaban kasar Muhammadu Buhari da suka boye sunayen su sun ce ba da sanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari aka sauke tsohon Sifetan ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ba.

Makusantan Shugaban kasar sun saki bayanan cewa bayan tafiyar Shugaban kasar Burtaniya an gudanar da wani bincike bisa jagorancin Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo inda aka gano cewa bayan cikar wa’adin tsohon Sifetan ‘yan sandan an kama shi da bada cin hanci na wasu biliyoyin kudi ga wasu masu ruwa da tsaki a fadar Shugaban kasar don su shiga su fita a tabbatar masa da Karin wa’adin.

Hakan ce tasa bayan kammala binciken aka mikawa shi Mataimakin Shugaban kasa sakamakon shi kuma ya Mara baya aka aiwatar da hukuncin sauke tsohon Sifetan ‘yan sandan Muhammad Adamu, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Daga Kabiru Ado Muhd

0 thoughts on “Babbar magana: Ba da sanin Buhari aka sauke tsohon sufeton ‘yan sanda ba – In ji wata Majiya.

 • April 7, 2021 at 9:04 pm
  Permalink

  Allah ya kyauta amma indae ankama shi da bada qalar naira biliyan biyu daya bada cin hanci to naji dadin cireshi da akayi

  Reply
 • April 7, 2021 at 11:00 pm
  Permalink

  Mmmmmm Allah Ya Kare mu a kasanan, da duniya gabakidaya

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *