Boko Haram na Arewa, Shuwagabanni marasa tausayi sai na Arewa, Wasu malaman ma sun daina tsoron Allah, basa fadin gaskiya, wa’azin ma ya zama siyasa, cewar Matashiyar ‘yar siyasa Munira Sulaiman.

Munira Sulaiman Tanimu wata Matashiyar ‘yar siyasa ce ‘yar asalin garin Saminaka a jihar Kaduna. Munira Sulaiman Tanimu ta yi fice wajen taimakawa Mata da Kananan Yara.

Munira Sulaiman ta yi wasu kalamai masu jan Hankali ga daukacin Al’ummar Arewa, in da ta bayyanar da irin girman matsalolin da Arewa take fuskanta.

Munira tace “Boko haram na arewa, shuwagabanni marasa tausayi sai na arewa, garkuwa da mutane, yan ta’adda, karancin Ilimi, rashin makarantu masu kyau, rashin asibiti da kayan aiki, rashin aikinyi ga matasa, fyade kacha-kacha, Shaye-shaye, marayu na cikin mayuwacin hali, almajirai na cikin yunwa, masu bara ta ko ina, mutuwan aure kacha-kacha. Mune munafunci, Hassada, gulma, gasa da juna, nuna isa, rashin kunya, fadin rai, girman Kai, rashin hadin kai, komai dai na arewa.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, ya Allah ka shiga lamarin arewa. Babu cigaba a arewa, mata Kullum haihuwa mukeyi, wai shin muna tunanin halin da yaran nan namu zasu shiga idan sun fito cikin wannan yanayin, inna lillahi wa inna ilaihir rajiun.

Ya Allah mun tuba. Abun kullum tabarbarewa ya ke kara yi, mun kasa magana, mun kasa hada kai, mun kasa bada muryar mu aro har mucimma burinmu, sai noke-noke a bayan wayarmu muna rubuce rubucen banza da bazai je ko ina ba……!

Kai, jama’a Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah mun tuba. Shuwagabannin mu na arewa kuji tsoron Allah, amanar mutanen ku na rataye a wuyarku. Idan kuka kiyin komai yanzun, toh gobe yaran cikinku da jikokin ku, sune cikin tashin hankali.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, wai ko kun manta cewa mutuwa na kan kowa ne, ko kun san ranar taku? ya Allah, ka shiga lamarin-nan.

Wasu malaman ma sun daina tsoron Allah, basa fadan gaskiya, wa’azin ma ya zaman siyasa.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Arewa bama son muga wani namu ya cigaba. arewa ba ma tallata abun arziki sai na tsiya.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya Allah ka shiga lamarin nan. Ya Allah mun tuba, ya Allah ka dafa mana.

Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah ya jikan musulmi. Ameen.”

Munira Sulaiman ta rubuta wadannan kalamai ne a shafinta na Facebook mai suna Munira Sulaiman Tanimu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.