Rahotanni

Buhari ya ce Najeriya na son wadata kasar Burundi da man fetur

Spread the love

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na son wadata kasar Burundi da man fetur, inda ya yi alkawarin cewa kamfanin man fetur na Najeriya zai duba bukatar kasar na tallafin makamashi.
.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, Mr Buhari ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa ranar Talata yayin da yake karbar bakoncin manzon musamman na shugaba Evariste Ndayishimiye.

“A kan neman taimako a fannin samar da makamashi musamman man fetur da shugaban kasar Burundi ya yi, shugaba Buhari ya ce ya san yadda kasar ke fama da karancin makamashi, kuma ya yi alkawarin cewa zai samu kamfanin man fetur na Najeriya don duba bukatar.”

“A cikin ruhin hadin kai da ‘yan uwantaka na Afirka, Najeriya za ta tallafa wa (Jamhuriyar Burundi) ta hanyoyi daban-daban kamar yadda ya kamata,” in ji shi.

Alkawarin da Mista Buhari ya yi na tallafa wa Burundi da samar da mai ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya suka fara samun man da za su saya bayan da aka dade ana fama da karancin mai a kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button