Rahotanni

Da yawan matasan da suka kammala karatu a Nigeria basu da ƙwazon aiki idan an ɗauke su. ~Cewar Minista Pantami

Spread the love

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Ministan sadarwa a Nigeria, Dr Isa Ali Pantami yayi zargin cewa mafi yawan ƴan Nigeria waɗanda su ka gama karatu, ba sa iya gudanar da aikin da aka ɗauke su yadda ya kamata.

Ya kuma koka game da yadda matasa suka dogara da neman aiki daga gwamnati bayan kammala karatu, maimakon shiga kasuwancin da zai taimake su.

A cewarsa, ba za mu taɓa yin alfahari da irin ɗaliban da ɓangaren ilimi a Nigeria yake samarwa a kowacce shekara ba, idan har matasanmu ba zasu iya gudanar da ayyukan da aka ɗauke su yadda ya kamata ba.

Pantami ya bayyana haka ne yayin gudanar da bikin bayar da kyautar karramawa a wani taro da aka shirya ranar Talata a Jihar Katsina.

Ya kuma ƙara da cewa, babban abin takaici ne, duba da yadda matasanmu suke ɗorawa kansu damuwa wajen samun aiki a gwamnati bayan kammala karatu maimakon shiga harkokin kasuwanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button