Rahotanni

Dakarun sojin saman Najeriya sun kai harin bama-bamai ta sama kan farar hula a kusa da kan iyakar jihar Nasarawa da Benue

Spread the love

Jaridar The Gazette ta ce ta ga gawarwakin mutane akalla 47 da aka tabbatar kawo yanzu an kashe su, tare da binne gawarwakin mutane 27 cikin gaggawa domin yin daidai da tsarin addinin Musulunci.

Rundunar sojin saman Najeriya ta sake gudanar da wani aikin kuskure wanda ya yi sanadiyyar kona fararen hula da dama sakamakon harin bam da aka kai ta sama, kamar yadda shaidu suka shaida wa Peoples Gazette.

Lamarin da ya faru a daren ranar Talata, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin munanan harin da jiragen yakin sojojin suka yi a shekarun baya-bayan nan, ya faru ne a Rukubi, kusa da kan iyakar kudu da Benue a karamar hukumar Doma, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Akalla mutane 47 ne aka tabbatar da mutuwarsu musamman Fulani makiyaya yayin da aka kwashe da dama zuwa asibitoci daban-daban a Nasarawa da Binuwai, kamar yadda shaidu suka bayyana. Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya tabbatar da faruwar harin da yammacin Laraba, inda ya ce ana kokarin ganin an shawo kan rikicin da sojoji.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ya ce hare-haren da aka kai ta sama a yankin a daidai wannan lokaci na ‘yan fashi ne kawai. Sai dai ya kasa bayyana adadin ‘yan bindigar da aka kashe a yayin harin ko kuma wasu da aka samu hasarar rayuka banda farar hula.

Harin dai ya janyo cece-kuce tsakanin mahukuntan Binuwai da al’ummar Fulani a tsakanin jihohin biyu. Shaidu sun ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan da wasu gungun Fulani makiyaya suka je Binuwai domin karbo dabbobin da aka kama.

Bayan sun biya tarar kimanin Naira miliyan 27 sun fara tafiya zuwa sansaninsu dake Nasarawa kafin a jefa musu bamabamai.

Jaridar The Gazette ta ce ta ga gawarwakin mutane kusan 50 da aka tabbatar kawo yanzu sun mutu, inda kawo yanzu aka binne gawarwaki 27 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ba a dai san adadin shanu nawa aka yi asarar ba a harin bam din da sojoji suka kai.

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta sha suka a shekarun baya-bayan nan kan yadda ta saba yin katsalandan a yayin gudanar da ayyukan korar ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da sauran masu aikata muggan laifuka daga dazuzzukan kasar. A kalla hare-haren bama-bamai da aka kai akalla takwas a kan fararen hula, ciki har da wasu da suka halarci wani daurin aure a Neja a shekarar da ta gabata, rundunar sojin Najeriya ta dauki alhakin kai harin ne tun a shekarar 2017, lamarin da ya kawo karshe ba tare da samun wani jami’in da ya dauki alhakinsa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button