Dalilin da yasa Ummi Zee Zee tace za ta kashe kanta wani Inyamuri ne ya damfareta Miliyan 450.

Tsohuwar jarumar kannywood Ummi Zeezee ta ce dalilin da yasa ta shiga kuncin rayuwa har tace za ta kashe kanta shine damfarar da wani Inyamuri yayi mata ta tsabar kudi har naira miliyan 450.

Ummi Zeezee ta ce Inyamurin ya ce zai sakata a harkar kasuwancin danyen man fetur ne, shi yasa yayi nasarar damfararta wadannan makudan kuadade.

Unmi Zee Zee ta fadi hakan ne a zantawarta da sashin Hausa na VOA.

Tace “Wani Inyamuri ne ya damfare ni har naira miliyan 450 kan cewa zai sakani a harkar kasuwancin danyen man fetur, yanzu kuma na nemi inda yake na rasa, shi yasa nace zan kashe kaina saboda takaici.” In ji Ummi Zee Zee.

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai tsohuwar jarumar ta kannywood Ummi Zee Zee ta bayyana cewa ta so ta kashe kanta saboda takaici da kuncin rayuwa da take fama dashi, inda tanemi jama’a su tayata da Addu’a.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *