Duk Masu Cewa Akwai Yunwa A Najeriya Makaryata Ne, In Ji Babban Na Kusa Da Buhari.

Daya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne.

Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels.

Dan siyasan yace a jiharsa na Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya. Yayinda aka yi masa tambaya game da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace:

Bana tunanin gaskiya ne saboda jihata da sauran jihohin Najeriya mutane basu jin yunwa.

Karya ce kawai, a kasar nan babu yunwa.

Daga Amir sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.