Duk wanda ya yada labarin cewa ina neman mijin aure ya cuceni, saboda ya jawo kowane Tom and Jerry yana turomin da hotonsa ta Whatsapp, in ji Ummi ZeeZee.

Tsohuwar jarumar fina finan Hausa Ummi Ibrahim, wadda akafi sani da Ummi ZeeZee ta koka kan yadda wani yarubuta labarin karya akanta, yace wai tana neman mijin aure.

Ummi ZeeZee ta ce ita dai tana da saurayinta wanda zata aure, kuma suna son junansu ita dashi, amma abin mamaki kawai sai aka sami wani ya je ya zauna ya rubuta karyar cewa tana neman mijin aure.

Ummi ZeeZee ta ce wanda yarubuta labarin cewa tana neman mijin aure ya cuceta, saboda ya jawo zubewar mutuncinta da kimarta, saboda kowane Tom and Jerry sai ya turo mata da hotonsa ta Whatsapp wai yana son zai aureta.

Ummi ZeeZee ta roki wanda yarubuta labarin da ya dubi girman Allah kada yasake rubuta wani labarin makamancin haka agareta.

Ta kara da ce da zaran ta bude Whatsapp dinta saƙonni ne suketa ambaliya, saboda yawansu bata iya karantawa.

Ummi ZeeZee ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *