Gobe za a yi muƙabala tsakanin malaman jihar Kano da malamin daya ke auren aljana

Gobe za a yi ta, ta ƙare

A gobe ne idan Allah ya amince gwamnatin Kano, karkashin ma’akatar addinai zata gabatar da titsiye ko Muqabala da Malamin nan ɗan asalin kofar Na’isa wanda yake da’awar ya auri aljana.
Wannan malami yace tun yana goye mahaifiyar sa ta fada dashi rijiya daga nan ne aljanu suka dauke shi suka cigaba da shayar dashi, Har ya girma, kuma yanzu haka ya auri aljana Umm Subyan ‘yar sarkin aljanu Har ta Haifa masa’ ya’ya.

A saboda Haka ne aka shirya zama da wannan malamin aljanu domin rarrabewa da baccin makaho.

Kamar yadda babban ɗan jaridar gidan rediyon Freedom radio Nasir Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *