Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed yayi kira ga kwamitin ƴan Majalisa domin a ƙirkiri sabuwar Jihar Katagum.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed yayi kira ga kwamitin ƴan Majalisar wakalai domin su duba yiwuwar ƙirƙirar sabuwar Jihar Katagum wadda a halin yanzu take ƙarƙashin Jihar Bauchi.

Gwamnan ya miƙa wannan ƙudiri ga kwamitin ƴan Majalisar wakalan ne jiya Litinin, yayin wata ziyara ta musamman da tawagar ta kai masa a fadar Gwamnatin Jihar Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana tare da miƙa ƙoƙon bararsa ga Wakilan domin tabbatarda an samar da sabuwar Jihar ta Katagum, bayan da ya bayyana yankin na Katagum a matsayin gunduma ta biyu mafi girma a Arewacin Nigeria, tare da nuni da cewa yin hakan zai ƙara kawo cigaba a rayuwar al’umma musamman mazauna yankin.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito yadda ƴan Majalisar suka kai ziyarar ga Sanata Bala Mohammed kwanaki kaɗan da ake shirye-shiryen fara gabatar da shirin jin ra’ayoyin Jama’a dangane da yunƙurin da ake na yiwa kundin tsarin mulkin ƙasa kwaskwarima.

A yayin nasa jawabin, Hon Aminu Suleiman wanda shine Shugaban kwamitin ƴan Majalisar, kuma shi ne ya jagoranci tawagar yayin ziyar; ya bayyana cewa babbar manufar wannan aiki na jin ra’ayoyin jama’a shine domin sanin irin matsalolin da suke addabar al’umma musamman a loƙacin da ake ƙoƙarin kyautata rayuwar al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Hon Aminu Suleiman ya ƙara da yabawa Gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Bala Mohammed bisa ga irin aikin alkhairi da take shimfiɗawa a faɗin Jihar domin kyautata rayuwar al’umma, “tare da yin alƙawarin cewa zasu gabatar da kuɗirin na Gwamna Bala Mohammed a yayin zaman majalisa wanda zai gudana kwanaki kaɗan masu zuwa.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *