Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Wa’adin Makonni Biyu A Dokar Kulle A Fadin Kasarnan.

Daga Miftahu Ahmad Panda

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Amince Da Karin Wa'adin Makonni Biyu A Dokar Kulle A Fadin Kasarnan.

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Boss Mustapha , shine yabayyana Hakan a Jawabin Da ya Gabatar Kan Kokarin Da Gwamnatin Tarayya takeyi Domin Ganin Ta Dakile Yaduwar Cutar Covid - 19 a Fadin Tarayyar Kasarnan a Ranar Litinin, 

Dokar Kullen Dai ta fara ne Daga Karfe 12 Na Daren Litinin (18 - Mayu - 2020) Zuwa Ranar 1 Ga Watan Yuni Mai Kamawa,

Idan Baku Mantaba a Jawabin Da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Gabatar a Ranar 27 Ga Watan Aprilu, ya Amince Da Sassauta Dokar Kulle A Birnin Tarayya Abuja, Tareda Jihohin Lagos Dakuma Ogun, Bayan Da Suka Shafe Tsawon Makonni 5 a Cikin Dokar Ta Kulle.

To Mudai Talakawa Sai Muce Allah ya Sassauta Mana, Domin kuwa Mafi Yawan Al'ummarmu Na Arewacin Najeriya Talakawa ne Wadanda Sai sunfita Suke Iya Samo Abinda Zasuci a Wannan Ranar.

Shin Ko Menene Makomar Irin Wadannan Al'ummar da basu da Cin Yau Ballantana na Gobe ?.

Leave a Reply

Your email address will not be published.