Rahotanni

Jami’an DSS sun harbe soja har lahira..

Spread the love

Wasu jami’an DSS da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun harbe wani soja mai suna Private Obafemi Adetayo har lahira a unguwar Lekki da ke jihar Legas.

An tattaro cewa Adetayo an harbe shi ne a cikin kimanin makonni uku da suka gabata a lokacin da ya yi yunkurin fitar da katin shaidarsa daga aljihunsa.

Sai dai wanda lamarin ya rutsa da shi tun bayan faruwar lamarin, ya rasu ne a ranar Litinin.

Wata ‘yar uwa, wacce ta wallafa lamarin a shafinta na Twitter @just_adulting_, ta bayyana cewa wanda aka kashe din ya mutu ne bayan yunkurin ceto rayuwarsa.

Ta rubuta, “Na rasa ɗan’uwa yau. Ya kasance Soja. Boko Haram ba su kashe shi ba, ‘yan bindiga ba su kashe shi ba. Bai mutu a fagen yaki ba. Jami’an DSS sun harbe shi a ciki a Lekki lokacin da ya yi yunkurin fito da katin shaidar sa.

“Rayuwa a Najeriya daidai yake da tafiya akan lokacin da bam zai tashi a minti na gaba. DSS ne suka kashe Peter. Ya yi kokarin kare kansa da kuma rike matsayinsa na soja ta hanyar fito da katin shaidarsa amma wannan yunkurin ne ya yi sanadin mutuwarsa.

“An harbe shi ne a ciki da wuri lokacin da ya yi yunkurin fito da katin shaidarsa. Ya rasu ne a asibiti kwanaki bayan yunkurin ceto rayuwarsa da bai samu nasara ba. Har ila yau, Nijeriya ta kasa nata. Ƙasar da yake ƙauna, ya bauta wa, ya yi yaƙi, an kashe shi. Ba ma a fagen daga inda ya yi yaki ya ci nasara ba, a kan titi.”

Mai magana da yawun runduna ta 81 na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Olaniyi Osoba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano halin da ake ciki a mutuwar wanda aka kashe.

Ya ce, “An harbe daya daga cikin sojojin mu a unguwar Lekki, kimanin makonni uku da suka gabata, kuma nan take muka samu labarin, sai aka dauke sojan domin a duba lafiyarsa, kuma tun a lokacin ba ya hayyacinsa yayin da ake gudanar da bincike amma abin bakin ciki mun rasa shi da safe amma duk da cewa mun rasa shi, za a ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button